Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Super Eagles Zata Kai Labari -Inji Amaju Pinnick


Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya bayyana cewar yana da kwarin gwiwar cewa kungiyar wasan kwallon kafa ta Super Eagles zata sami nasarar shiga gasar wasan cin kofin duniya na kasashen Afirka da za’a buga a shekarar 2017 da kuma kofin duniya na hukumar FIFA a shekarar 2018.

Najeriya zata kara da Egypt a watan maris na wannan shekarar domin tantance rukunin shiga gasar zakarun cin kofin na AFCON na shekarar 2017 da za a buga a kasar Gabon.

A cikin watan goma na wannan shekarar ne za a fara buga wasan shiga gasar cin kofin duniya na FIFA na shekarar 2018 wanda za a buga a kasar Rasha.

Shugaba Pinnick a jawabin sa ta kafar talabijin ya jinjinawa kungiyoyin ‘yan wasa da dama da suka yi fice a shekarar 2015.

Amaju Pinnick ya jaddada cewa “wannan nasara ba ta mutum guda bace kawai, su kansu mambobin wannan kwamitin sun taka rawar gani, kuma lallai kan mu a hade yake”.

Nasarar da ‘yan wasa masu kasa da shekaru 20 suka samu a Senegal, da ‘yan kasa da shekaru 17 a kasar Chile, da kuma ‘yan kasa da shekaru 23 na kasar Senegal, da kuma nasarar shiga gasar rukunin B na zakarun ‘yan wasan Afirka da kungiyar ‘yan wasan Super Eagles suka yi na nuna irin hazaka da mayar da hankalin kungiyoyin.

Daga karshe shugaban ya kara da cewa “ina da kwarin gwiwar cewa bana sai tafi bara, ganin yadda kungiyar ‘yan wasan Super eagle za su shiga gasar cin kofin zakarun Afirka na shekarar 2017, da kuma fara shirye shiryen zuwa cin kofin duniya na shekarar 2018.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG