Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanne Irin Kalubale Samari Da 'Yan Mata Ke Fuskanta Wajen Zaben Miji Ko Mata?


Shirin samartaka na dandalin voa ya sami zantawa da samari da ‘yan mata da dama domin jin ra’ayoyin su akan irin kalubalen da yawancin su ke fuskanta musamman a lokacin da suke kokarin zabe ko tsayar da maza ko matan da zasu aura.

A tattaunawar mu da samari, yawanci babbar matsalar da suka koka akai ita ce irin rawar da wasu daga cikin ‘yan uwan budurwar da suke niyyar aura ke takawa.

Yawancin kalubalen kamar yadda wani daga cikin matasan ya bayyana mana shine, bayan budurwar ta amince da shi, har sun fara shirye shiryen auren aure sai kwatsam daya daga cikin kanen innar ta, ta kawo wani saurayi wanda sauran ‘yan uwan suka nuna lallai sai shi zata aura.

Da tafiya tayi tafiya, saurayin ya bayyana cewar bai san lokacin da suka hure mata kunne ba domi kuwa ita da kanta ta kira shi ta bayyana masa cewar bazata iya zama da shi ba.

Akwai matsaloli da dama makamantan rashin abin hannu, da kwadayi, da sauran su wadanda suke kalubalantar matasa maza da mata a lokacin da suke kokarin zabar abokan zaman su.

Saurari cikakken bayanin a nan…Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG