Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan-Wasa Thierry Herry Yace Kungiyar FIFA Tana Hauka Ne?


Shahararren Dan-wasannan Thierry Henry yace lallai wannan zai iya zama hauka idana har akace fittaccen dan wasannan Lionel Messi bai samu lashe tagullar zinariya ta lambar yabo na Ballon D’or ba.

A ranar litini mai zuwa ne ake sa ran hukumar kwallon kafar duniya FIFA zata bayyanar da fitaccen danwasa na shekarar 2015 wanda za’ayi a garin Zurich, inda ‘yan wasa 3 suke gogoriyar neman lambar yabon Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo.

Mai tsaron gida dan kasar Argentina shi akafi tsanmanin zai iya lashe wannan lambar, kana dan wasa Henry, yana bashi goyon bayan don samun wannan kyautar a karo na 5, duk dai dacewar ya nuna rashin jin dadinshi a rashin dan wasa Luis Suares.

Dan wasa Henrry, ya bayyana a shafin hukumar kwallon kafar Barcelona, cewar babu abun da zamu iya yi, illa dai su ji dadin abun da dan wasa Messi yayi, domin kuwa abubuwan da yakeyi sun shahara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG