Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aure Ko Haihuwa Baya Hana Ilimi


A shirin mu na wasu mata da suka taka muhimmiyar rawa a alummarsu a yau mun sami zantawa da malam Hassana Abubakar.

Hassana Abubakar dai ta yi karatunta na boko tun daga kan firamare har sakandare a garin Kano inda ta karanci aikin jarida, a digirin farko.

Hassana ta koma makaranta inda ta kara digirin ta na biyu , a fannoni daban daban har guda uku, kuma duk wannan fadi tashe da tayi na batun karatu tana da aure da 'yaya.

Ta kara da cewa duk wannan hadin kai da taimakon mijinta shine ya bata damar cimma wannan nasarar, ta kuma bukaci mata dasu tashi tsaye wajen neman ilimi cewa aure ko haihuwa baya hana ilimi.

Ta kuma samu nasarori da dama ta sanadiyar ilimin karatun boko da aikin ta , domin a cewar ta, ta samu damar zuwa kasashen turai har guda biyu ciki har da kasar Jamus.

XS
SM
MD
LG