Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayne Rooney Ya Kafa Tarihi a Ingila


 Wayne Rooney
Wayne Rooney

Dan wasan gaba na Manchester United Wayne Rooney, ya lashe kanbin dan wasan da yafi kowa taka leda a kasar Ingila, a karo na 4, bayan da ya kuma kafa abun tarihi wajen jefa kwallaye a raga.

Rooney, dan shekaru 30, ya jefa kwallaye 51, fiye da Bobby Charlton, wanda ya dade babu wanda ya kamo shi sai a wannan karon da Rooney yayi masa fintinkau, sun kuma samu nasarar shiga gasar Tarayyar Turai na shekarar 2016.

Rooney, Kaftin din kasar Ingila ya sami kashi 37, cikin 100, na yawan kuri’un da aka jefa , kuma ya taba, lashe wannan kanbi a shekarun 2008, 2009 da 2014.

Mai tsaron gidan Stoke City, Jack Butland, wanda shima ya nuna bajinta a kakar wasan shi aka zaba a matsayin wanda yazo na 2, za’a mika masu Kyautarsu a ranar 26, ga watan Maris, a kasar Jamus.

XS
SM
MD
LG