Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Pillars Ta Sallami 'Yan Wasa Goma


Tambarin Kano Pillars
Tambarin Kano Pillars

A wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Idris Malikawa ya fitar a hirar sa da manema labarai yau talata, kungiyar ta sallami ‘yan wasa goma a shirye shiryen da take yin a shiga sabuwar kakar wasanni ta shekarar 2016.

Malikawa ya bayyana cewa an salami ‘yan wasanne a sakamakon wasu dalilai dake da nasaba da lafiya, da kuma kwarewa cikin aikin ayyukan su.

Ya kara da cewa, hukumar kungiyar kwallon ta yanke shawarar yin hakanne domin a ganinta hanyar kadai da kungiyar zata iya bi domin gyara kurakuran da ta fuskanta a daga farko zuwa karshen wannan kakar.

Malikawa ya bayyana cewa yanzu haka dai kungiyar ta fara shirye shiryen horas da wasu sababbin ‘yan wasan da zasu maye gurbin guda goman da kungiyar ta sallama.

A danna Dandalinvoa.com domin jin cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG