Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kannywood Na Taimakawa Wajen Samarda Aiki Ga Matasa


Sani Sule Katsina Kannywood
Sani Sule Katsina Kannywood

A shirinmu na nishadi a yau mun sami bakunci wani mai shirya fina finai da ya shafe shekaru tara yana harkar fim, Sani Sule Katsina ya ce sha’awa ce ta sa ya bar aikin gwamnati domin shiga harkar fina finai.

Ya ce yana shirya fina finai na series wato, jerin fina finai da ake sawa na tsawon lokaci, yana kuma yin TV talkshow na Hausa wadanda ake sa wa a gidajen talabijin da ma gidajen sinima.

Ya kara da cewa karuwan gidajen Talabijan na gida da waje da kuma gidajen Sinima, yasa bukatar neman fina finai ya karu.

Sani Sule, yana mai cewa masu harkar fina finai na taimakawa gaya wajen samowa matasa aiki yi, saboda haka ya kamata Gwamnati ta kamakawa masu wannan harka domin kara taimakawa matasa.

XS
SM
MD
LG