Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Saurayi Ya Shake Jariri Har Lahira


Wani saurayi dan shekara ashirin da biyar Abubakar Ibrahim mai sana’ar saida tabar wiwi ya shake wuyan jariri mai watanni biyu da haihuwa har lahira a birnin Jalingo fadar jihar Taraba.

Malama Karshe Hamuel ta shaidawa wakilin sashin Hausa cewa ta jefawa uban jaririn sakamakon kasawa da ya yi na sauke hakkinsa na uba watanni biyu bayan haihuwarsa. Amma juyawarta ke da wuya sai ta ji jaririn na kuka, wanda ta tarar yana rugume da shi ba rai.

Kawun uwar jaririn Rev. John Hosea wanda ya tabbatar da abkuwar al’amarin yace kamata ya abin da ya sami Malama Karshe ya zamo isshara ga sauran ‘yan mata da ke gararamba akan layi da samari.

Halin da ake ciki dai Abubakar Ibrahim yana hanun ‘yan sanda inda suke tatsar bayanai daga gare shi inji jam’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda na jihar Taraba DSP Joseph Kwaji.

Ga Sanusi Adamu dauke da cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG