Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An ba Priyanka Chopra Kambin Yabo a Amurka


Shahararriyar tauraruwar ‘yan wasn nan ta Indiya Pyrianka Chopra ta sami kambin yabo a wata Gala ta shekara shekara da ake yi a Amurka.

Priyanka Chopra ta zamo ‘yar wasa ta farko da ga kudancin nahiyar Asiya da ta taba samun irin wannan kambin da ake kira People's Choice Award a turance. An bata lambar yabon ne saboda fice, da taka rawar da ta yi a wani wasa da ake nunawa a talabijin mai suna "Quantico" inda ta fito a matsayin jami’ar bincike.

Tauraruwar ‘yar shekaru 33 da haihuwa, wadda ta ke daya daga cikin taurarin ‘kasar Indiya da ake ji dasu, ta doke takwarorinta kamarsu Emma Roberts, Jamie Lee Curtis, Lea Michele da Marcia Gay Harden.

Priyanka ta sanya hoton ta dauke da kambin da aka bata a shafin twitter, ta kuma godewa magoya bayanta don zaben ta da su ka yi, ta na mai cewa “ta taki sa’a”.

Da ta ke bayani game da Galar, Priyanka ta bayyana bukin a matsayin wani sabon abu a gareta, kasancear shine karon ta na farko da samun irin wannan kambin. Ta ce amma abin mamaki shine yadda mutanen da ba ta sani ba su ka zo su ka gaishe ta suka kuma kai ta wajen wasu mutanen. Ta kara da cewa, abin yayi kyau sosai kuma jama’ar wurin sun kyautata mata.

XS
SM
MD
LG