Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samba Gwabba Zata Kece Raini Da Hasla FC A Bauchi PFA Cup 2017 (1st Edition )


A tarayyar Najeriya cikin jihar Bauchi, kungiyar matasa masu son cigaba na kwallon kafa mai suna Bauchi Progressive Football Association, ta saka gasar cin kofi na Kungiyoyin kwallon kafa na matasa a fadar jihar a karon farko Mai taken Bauchi Progressive football Cup 2017 (1st Edition).

Kungiyar tace wanna gwaji ne za tayi ta kuma ce ta saka wannan gasar ne domin jawo hankalin matasa da kuma masu ruwa da tsaki bangaren wasannin tamola dan ganin an taimaka wa matasanmu su samu shiga wasu kungiyoyin kwallon kafa masu buga lig daban daban kama daga cikin gida har zuwa wasu jihohi dama wasu kasashen waje.

Za'a buga wasanne tsakanin Kungiyoyin kwallon kafa har guda goma na cikin garin Bauchi, inda za'a Fara bude wasan tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Samba Gwabba, da ta kwararta ta Hasla FC, dukkansu daga cikin garin Bauchi.
Ranar Lahadi 8/1/2017 a filin wasa na tunawa da Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa dake cikin garin na Bauchi, da misalin karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya Da Nijar.

Ana sa ran manya manyan baki daga bangaren gwamnati da wasu fitattun tsofaffin 'yan wasa kwallon kafa na kasa zasu samu halartar wannan gagarumin wasan da Kungiyar Bauchi Progressive football ta shiya a karon farko.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG