Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Na Cika Shekaru 50 Kafin In Bar Kwallon Kafa (Zlatan )


Tsohon dan wasan gaba na kasar Sweden, wanda a yanzu yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Zaltan Ibrahimovic, yace yana da kwarin guiwar da zai cigaba da taka leda har nan da shekaru sama da goma masu zuwa

Zaltan dan shekara talatin da biyar da haihuwa ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, a farkon kakar wasan bana

Bayan da kwantiraginsa ya kare daga kungiyar PSG, ta kasar Faransa, inda ya rattaba hanu na tsawon shekara daya don takawa Kungiyar ta Manchester leda

A yanzu haka Ibrahimovic ya jefa kwallaye har guda goma Sha daya a gasar firimiya ta bana.

A na sa ran zai sake tsawaita kwantiraginsa a Manchester united.

Shima mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta kasar Italiya Wanda a yanzu haka yake kama wasa a kungiyar Juventus Buffon, yace bashi da niyar ajiye takalman wasansa sai ya cika shekaru 65 da haihuwa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG