Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Da Wasu Kungiyoyi Sun Sa Fam Miliyan £35 Kan Anderson Talisca


Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United, ta ce zata iya amincewa mai tsaron ragarta David De Gea, mai shekaru 27 da haihuwa ya koma kungiyar Real Madrid, a kakar wasan bana amman idan ita Manchester ta samu nasarar sayen mai tsaron raga na Atletico Madrid, mai suna Jan Oblak.

Har Ila yau Manchester United tare da wasu kungiyoyin kwallon Kafa guda biyu wadan da ba'a bayyana sunansu ba daga kasar Sin, sun jera sahu guda wajan zawarcin dan wasan tsakiya na Benfica, mai suna Anderson Talisca, dan shekaru 24 a duniya inda duka kungiyoyin suka sanya fam miliyan £35 kan sayen dan wasan dan kasar Brazil,

Sasantawa tsakanin Manchester United da takwararta Tottenham kan batun sayen dan wasan baya na Tottenham Toby Alderweireld, mai shekaru 29 ya rushe sakamakon kungiyar Tottenham tana bukatar kudin da ya kai fam miliyan £55 daga hannun Manchester United kafin ta sake danwasan dan kasar Belgium.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG