Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zawarci Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa


A cigaba da saye da sayarwa da ake yi na ‘yan wasan kwallon Kafa ta duniya.

Kungiyar kwallon Kafa ta Lyon dake kasar faransa ta ce zata amince wa dan wasan gabanta, mai suna Nabil Fekir, dan shekaru 24 a duniya da ya koma kungiyar Liverpool a farkon kakar wasan bana amma idan an saye shi bisa farashin da ya dace.

Manchester City, zata biya zunzurutun kudi har fam miliyan £43 wajan ganin ta sayo dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli mai suna Jorginho dan shekara 26 da haihuwa wanda tuni wikilinsa yake kasar Ingila domin kammala cinikin a karshen makon nan.

Da yuwuwar kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta yi zawarcin mai horas da kungiyar Chelsea Antonio Conte, domin yazo ya maye mata gurbin tsohon kocinta Zinedine Zidane wanda ya ajiye aikinsa kwatsam a satin da ya gabata.

Tottenham zata biya fam miliyan £48 wajan sayen matashin dan wasan baya daga kungiyar Ajax mai suna Matthijs de Ligt, dan shekara 18 da haihuwa.

Manchester United, ta kammala sayen matashin dan wasan baya mai suna Diogo Dalot, mai shekaru 19 da haihuwa daga kungiyar FC Porto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG