Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Broncos Ta Lashe Wasan Super Bowl Karo Na 50


Carolina Panthers’ Cam Newton, left, talks to Denver Broncos’ Peyton Manning (18) after the NFL Super Bowl 50 football game Sunday, Feb. 7, 2016.
Carolina Panthers’ Cam Newton, left, talks to Denver Broncos’ Peyton Manning (18) after the NFL Super Bowl 50 football game Sunday, Feb. 7, 2016.

A jiya Lahadi ne aka yi karon karshe na gasar shahararriyar kwallon Zari Rugar nan ta Amurka karo na 50. Wacce aka kara tsakanin kungiyoyin wasannin Denver Broncos da Carolina Panthers, inda Denver Broncos suka ci gasar a karo na 3 a tarihinsu da ci 24 da 10 a tsakaninsu.

An yi matukar samar da tsaro da kowa ka iya ganewa idanunsa a tsakanin Otal-Otal zuwa filin wasan Levi Stadium dake Santa Clara ta jihar San Francisco inda buga wasan. Hatta irin ababen daukar Bidiyon da ake tadawa sama ana sarrafa su suna hoto ba a yarda sun tashi sama ba a unguwar.

Ba a ma yarda da kallon wasan a gidajen kallon da zai dauki mutane da yawa ba, kamar yadda aka yi a manyan wasannin kwallon Kulki ba a shekarun 2010, 2012 da kuma 2014 ba.

Wannan wasa an yi matukar kawata shi ta inda makada da mawaka suka baje kolinsu kafin a dawo hutun rabin lokaci, inda mawakiya Beyoncé da Mawaki Bruno Mars suka cashe a filin wasan.

XS
SM
MD
LG