Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwarzuwar Boxing Laila Ali Tayi Tsokaci Akan Wasan Rousey Da Holly


Fittacciyar ‘yar wasan Boxing kuma babbar ‘yar shaharareen wasan Boxing na duniya Laila Ali, wadda ta bar wasan boxing, tayi tsokaci akan wasan da aka gwabza tsakanin maccen da tafi kowace mace karfi a fagen boxing Ronda Rousey ta duniya, wanda Holly Holm tayi nasara a kanta.

Laila Ali, tace gaskiya tana ganin cewar babu yadda Rousey zatayi da Holly, domin kuwa wannan lokacin ta ne, sai dai tayi hakuri. Idan kuma suka sake hadduwa babu yadda za’ayi ta iya yin nasara akan ta. Ta kara da cewar ai tun a zagaye na 2 fa akayi nasara akan Rousey, wannan na nuna maka cewar abokin hamayar ka yafi karfin ka kenan, idan har tun ba aje ko ina ba ya fitar da kai.

Laila Ali, tace ai Rousey wasanni 12 kawai tayi, kuma akwai wasu mata da suka fita karfi, amma tana ganin cewar Holly, mace ce da take ganin cewar tana da karfi. Laila ta kara da cewar, ni gaskiya ban hadu da Holly ba a baya, amma nasan takai mace. Yanzu haka dai a ranar Laraba mai zuwa ne zasu sake gwabzawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG