Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sunday Oliseh Da Alamun Ta Leko Kuma Zata Koma


Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) tace zai iya kasancewa ta dakatar ko kuma rage wa babban kocin ‘yan wasan Super Eagles Sumday Oliseh girma biyo bayan irin kalaman da ya yi bayan doke kungiyar ‘yan wasan da abokiyar karawar ta ta yi a wasannin zakarun cin kofin nahiyar Afirka (CHAN).

Jami’an hukumar sun bayyana cewar babban kocin na neman wuce makadi da rawa bayan rashin tabuka abin kirkin da ‘yan wasan suka yi a Ruwanda.

Oliseh ya dora laifin rashin kwazon ‘yan wasan nasa akan rashin cikakkiyar kulawa dasu, Kocin ya kara da cewa saida ya cire kudi daga aljihunsa dalar Amurka dubu hudu sa’annan ya dauki dawainiyar kula da ‘yan wasan a yayin da suke gudanar da horo kafin wasan.

A cewara daya daga cikin jami’an a hirar su da jaridar all sport, maimakon Oliseh ya dauki laifin rashin ntabuka abin kirkin da ‘yan wasan suka yi, sai ya dora laifin ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya wai har ma yana cewa rashin kulawa da karfafa masu gwiwa ne yasa haka.

Ya kara da cewa yanzu haka suna jiran kocin ya mayar da martanin takardar da suka rubuta masa ne kafin hukumar ta yanke hukuncin matakin da zata dauka akan sa, zata iya kasancewa mu mayar da shi karkashin mai bada shawarar tawagar ‘yan wasan ko kuma ya aje aiki domin a cewar jami’in, baza su iya barin shi ya cigaba da wasa da hankalin kungiyar ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG