Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingila Zata Yi Rashin Alex Iwobi Inji- Arsene Wenger


Manajan kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce lallai Ingila zata yi rashin fitaccen dan wasa Alex Iwobi, wanda yace ya gwammace ya bugawa Najeriya wasa a fagen wasanni na kasa da kasa.

Dan wasan mai shekaru goma sha tara da haihuwa ya sake taka rawar gani a yayin da kulob din Gunners ya lallasa Burnley da ci 2-1 a wasan FA zagaye na hudu da aka buga ranar asabar da ta gabata.

Wenger ya fadawa mujallar Mirror cewar lallai ingila zata yi matukar rashin wannan dan wasa da ya zabi ya bugawa Najeriya wasa a maimakon ingila.

Wenger ya kara da cewa ya tuna kokarin da yayi domin tura dan wasan ya buga wasan kawance na ‘yan kasa da shekaru 23, sai kwatsam Najeriya ta kira shi.

Daga karshe Aresn Wenger ya ce, babu yadda za’a yi dan wasa ya juya wa kungiyar sa ta fari baya, Najeriya kasa ce mai dinbin tarihin masoya kwallon kafa, kamar Okocha da Kanu Nwanko ma ai duk daga can suka fara.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG