Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakiyar Nan Celine Dion Ta Shiga Takaba


Kamar anyi ruwa an dauke. Shahararriyar mawakiyar nan “Celine Dion” ta bayyana a cikin jama’a. Ita dai mawakiyar mai shekaru 47, ta dade babu wanda yasan irin halin da take ciki. Amma a ‘yan kwanakin nan ta rubuta a shafin ta cewar.

Ina kara yima masoyana godiya da sakon ta’aziyya da suke ta aiko mun, tun bayan rasuwar mijinta Mr. Rene Angelil, a ranar 14 ga watan Janairu mijin nata mai shekaru 73, ya mutu ne bayan jinya da yayi na rashin lafiyar ciwon daji. Ita dai mawakiyar ta bayyana a lokacin jana’izar mijin nata tana sanye da bakaken kaya tare da tagwayen ‘yayan ta ‘yan shekaru 5.

Sun dai kwashe samada shekaru 20 da yin auren su, haka kuma takara da cewar tana mika godiyar ta ga gwamnatin kasar Quebec, da suka taimaka da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki a ka gudanar da bukin birne mijin nata. Haka kuma wannan abubuwan sun hade mata duk a lokaci daya, domin kuwa kwanaki kadan bayan rasuwar mijin nata sai kaninta Daniel, shina ya mutu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG