Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Boxin Mata Ma Ba'a Barsu A Baya Ba!


Ronda Rousey
Ronda Rousey

Shahararriyar ‘yar wasannan na “Boxing” Ronda Rousey, ta dau alwashin bazata kalli video din wasan da suka gwabza da abokiyar hamayyar taba Holly Holm a watan Nowamba da ta gabata. Hasalima tana cewar bata ko bukatar tuna yadda wasan nasu ya kasance. Dalilin ta kuwa shine, tayi mamakin yadda akayi Holly ta iya yin nasara a kanta, don kuwa tana ganin cewar itace zakarar gwajin dafi na mata a fagen wasan boxing a duniya.

Koci din ta Mr. Edmond Tarverdyan, ya bayyanama gidan talabijin na ESPN cewar ‘yar wasan tashi bata kalli wasan ba, kuma bata da bukatar kallon wasan koma tuna yadda wasan ya kaya. Abun la’akari da shi a nan shine ba wai Ronda ta kalli wasan shine abu mai muhimanci yanzu ba. A’a aikin ya rage gareni na kalla wasan, don nagano makasar Holly, domin kuwa muna shirin sake haduwa da ita a nan gaba kadan.

Ana dai ta sukar koci din na Ronda, da cewar ai shine bai shirya ta yadda ya kamata ba, domin kuwa da tayi nasara. Ganin cewar bayan rasa nasara a wasan, sai gashi ya fito yana ta wasu maganganu da basu kamata ba a kan nasarar da Holly tayi a kansu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG