Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Da Shekarar 2050 Wata Sabuwar Duniyar Zata Fara


New Planet Nyptun
New Planet Nyptun

Shekaru na kara zama kwanaki, kwnaki na kara zama awowi, awowi na kara zama mintuna, rayuwa nakara zama wani abu. Abubuwa nata kara canzawa, wanda ada yadda ake gudanar da abubuwa musamman a wajajen aiki, za’a ga canje-canje da dama.

Yanzu har ankai ga lokacin da ma’aikata ke saka tsunman suke wuya da saka kaya iri daya, don zuwa wajen aiki. Bisa ga dukkan alamu nan da shekarar 2050 abubuwa zasu canza matuka, musamman yadda ma’aikatu ke gudanar da ayyukan su. Nan gaba kadan za’a iya kaiwa matakin da mutun-mutumi zai maye gurbin mutun a wajen aiki, don haka za’a shiga matsalar rashin aikin yi kenan. Sai dai kuma shi mutun-mutumin kan samar da wasu ayyuka da ba’a da su ada. Kamfanoni zasu fara daukar ma’aikata daga wasu kasashe na duniya, suna musu aiki ta yanar gizo, domin kuwa ta hakan zasu guje ma biyan kudade masu yawa, da biyan haraji.

Mutane da dama zasu daina barin aiki don yawan shekaru ko dadewa a aiki, haka kuma kamfanoni zasu fito da wasu tsare-tsare wanda zasu dinga bibiyar yadda ma’aikatan su ke gudanar da rayuwar su ko bayan offis. Haka kamfanoni zasu daina daukar manya-manyan gine-gine a matsayin ofisoshin su, sai dai su dinga amfani da gidajen su wajen gudanar da aikin ofis. Su kuwa motoci da basu bukatar direba, zasu yawaita da saukaka abubuwa ga mutane da dama. Wai shin wannan rayuwar ina zata kai mutane ne?

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG