Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morrocco Ta Saye Dan Wasan Kwallon Najeriya Domin Taka Leda


Kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors ta amince zata sayarda dan wasan ta Chisom Chikatara , akan zunzuruntun kudi dala Amurka, 700.000, kwatankwacin Naira miliyan 139, ga kungiyar kwallon kafa Botola Wydad Casablanca ta kasar Morocco.

Chikatara dai ya nuna bajinta da nuna cewa ya iya taka leda, a gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka, inda ya jefa kwallaye 4, a raga a wasani 3, koda yake kungiyar Super Eagles ta gaza tabuka abun arziki inda ta sha kashi a hannun Guinea da ci 1, mai ban haushe.

Kungiyoyin kwallon kafa da dama daga kasashen dake arewacin Afirka sun nuna shawarsu kan Chikatara idan daya daga ciki kungiyoyin suka yi tayi dalar Amurka 500. Amma hakarsu bata cimma ruwa ba.

Idan ya amince da ka’idojin kwantragin Chikatara zai rattaba hannu a kwantragin shekaru 3.

XS
SM
MD
LG