Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalla Milliyan $63 Na Cacar Lottery Haryanzu Babu Maisu!


Hukumar cacar jihar Califonia, ta bayyanar da rashin jin dadin su da har ya zuwa yanzu babu wanda ya fito don bayyanar da kanshi a matsayin wanda ya ci cacar dallar Amurka $63M dai-dai da naira billiyan goma sha biyu N12B.

A cewar shugaban hukumar Alex Traverso, sun yi mamaki na yadda har zuwa yau babu wanda ya bayyanar da kanshi a matsayin wanda yayi nasarar lashe wannan garabasar. Domin kuwa wadannan makudan kudin babu wanda zai so ace ya rasa su.

Yace doka dokace, duk wanda bai fito don ya bayyanar da kanshi a matsayin wanda ya lashe kudin nan ba, har zuwa ranar Talata mai zuwa, zai rasa wannan kudin, domin kuwa sun dade suna ajiye da kudin kimanin tsawon watanni 6 ke nan babu wanda ya fito.

Yace gaskiya yana gani idan dai da akwai wanda ya siya tikitin shiga wannan cacar, to ya hanzarda bincike gidan shi don neman wannan tikiti da ke dauke da lambar da tayi dai-dai da lambar cin gasar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG