Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Ousmane Dembele
Ousmane Dembele

A bangaren cinikaiyan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya. kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da takwararta ta Borussia Dortmund, na kasar jamus sun cimma yarjejeniya kan cinikn dan wasan gaba na Dortmund, mai suna Ousmane Dembele dan shekara 20 da haihuwa akan kudi fam miliyan £90, wanda zai maye gurbin Neymar da ya kuma kungiyar Paris Saint German daga Barcelona.

Manchester city, ta kudiri aniyar ganin ta dauko dan wasan gaba na Arsenal, Alexis Sanches, akan kudi fam miliyan £60, sai dai tuni dama mai horas da kungiyar ta Arsenal Arsene Wenger, ya ce ba zai saidai dan wasan zuwa wata kungiyar da take taka leda a kasar Ingila ba.

Shi kuwa Jagoran ‘yan wasan Liverpool (Captain) Jorda Henderson, ya ce zai yi kokarin ganin ya shawo kan dan wasan tsakiyarsu Philippe Coutinho, domin ya cigaba da zama a kungiyar, inda Barcelona ta sha alwashin ganin sai ta raba dan wasan zuwa kungiyar sai dai mai horas da kungiyar ta Liverpool ya ce ba na sayarwa bane.

Arsenal na zawarcin dan wasan Real Madrid, Marco Asensio., ana kuma sa ran cewa Zlatan Ibrahimovic zai dawo atisaye tare da Manchester United nan da awanni 24 masu zuwa inda ake zaton dan wasan zai sake rattaba hannun a kungiyar ta Manchester bayan kammala wa'adin sa na shekara daya da yayi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG