Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taimakawa Juna Nada Fa'ida Akwai Ma'aikata 30 A Kamfani Na


Adeshola Komalafe

Wata matashiya Adeshola Komolafe, ta ce ta ga mahimmancin dogaro da kai domin ta bude kamfanin da ya danganci aikin jarida wato intergrated market communication mai suna' media insight' da zummar gudanar da ayyukan bincike, aikin jarida da tallace-tallace mussamam ma ga kungiyoyi masu zaman kansa na gida da na waje ta hanyar samawa matasa aiki yi .

Adeshola ta ce tana da kimanin ma’aikata 30 da ke aiki a karkashinta inda kowanne ke da irin nasa aiki kama daga aikin daukar hoto, editin , bincike da ma sauransu.

Ta kara da cewa suna taimaka ma’aikatun gwamnatin ko kamfanoni wajen gudanar da horo ga ma’aikatansu domin inganta ayyukansu na yau da kullum.

Ta ce sukan samar da wasu shirye shirye da sukan sayarwa gidajen jarida idan bukatar hakan ta taso

Mai sauraro atara mako mai zuwa domin jin cigaban da hirar mu da ita domin jin gwagwamaya da aka sha kasancewarta ba yar arewa ba amma ayyukanta sun fi tasiri a arewancin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG