Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Ilimin Taurari, Sun Hango Karin Jariran Taurari 4


Masana kimiyya da fasaha a kasar Amurka da Birtaniya, sun samu nasarar gano karin wasu taurari hudu, wanda kadan suka fi girman duniya, mutun na iya ganin hasken su da kwayar ido.

Yin amfani da fasaha mai mahimmanci wanda zai iya auna ƙananan canje-canje a cikin hasken da wasu taurari sukan fitar, masana kimiyya a Jami'ar California Santa Cruz da Jami'ar Hertfordshire, sun gano taurari a kusa da tauraron Tau Ceti, wanda shine tauraro da ya kwashe tsawon shekaru 12, yana bada haske zuwa wannan duniyar.

Biyu daga cikin taurarin sararin samaniya, a yankin da ake kira wurin zama, suna nuni da cewar ana iya samun ruwa masu zurfi. Canje-canje da ake samu cikin haske, yana haifar da motsawa daga cikin taurari, ko yin amfani da tauraro.

A kudancin gefen tauraron nan Cetus, yakan fitar da hasken rana kamar rana, wanda yake da kusan kashi 25 cikin dari na hasken da akan samu a sararrin sama a kowane dare.

Tsakanin taurari biyu a yankin, wadanda girman su yafi girma fiye da duniya, suna rayuwar su ta dai-dai da dai-dai, duk dai da cewar masana rayuwar taurari na damun su, wanda hakan yake takurama rayuwar taurarin matuka

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG