Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mace Ta Farko A Kasar Pakistan Ta Zama Shugabar 'Yan Sanda


Rizwana Hameed shugabar 'yan sanda ta farko a kasar Pakistan
Rizwana Hameed shugabar 'yan sanda ta farko a kasar Pakistan

Kasar Pakistan, itace kasa ta biyu dake da yawan Musulmai a fadin duniya, kimanin kashi casa’in da shida 96% na al’umar kasar Musulmai ne. Hakan yasa wasu al’adar mutanen kasar suka banbanta da sauran kasashe a fadin duniya.

Rizwana Hameed, itace mace ta farko da ta kafa tarihi a kasar, inda ta zama mace ta farko da ta kai matakin shugabar wani bangare na Police, wannan wani abun kunya ne bisa ga al’adar kasar, a samu mace tana aikin ‘yar sanda.

A yanzu haka dai itace shugabar wani yanki a gidan ‘yan sanda, inda take shugabancin maza a yankin. Tace abu da ya kara mata karfin gwiwar shiga aikin tsaro, shine yadda mata da yawa ake take musu hakkin su, ko kuma a samu mata basa iya fadan damuwar su don neman musu hakkin su, kasan cewar, a duk lokacin da su kaje don magance wata matsala, sai suyi karo da maza ke tambayar su.

Saboda hali da al’adar su, mace tana da kunya, wajen bayyanar da kanta musamman akan wasu abubuwa da suka shefi rayuwar ta. Haka da yawa akan samu mutane da suke daukar cewar, aikin su kawai aikin zaman gida ne, ita tana da yakinin cewar, mata suna iya aiki kowane iri, ba kawai yadda aka dauke su da cewar su aikin gidane kawai nasu.

A nata fahimtar rayuwa shine, babu wani aiki da namiji zaiyi da basu iya yin shi, hasalima akwai aiki da mata kawai suke iya yi, kamar aikin renon yara, ba kowane namiji ne zai iya aikin ba, amma mata kuwa zasu iya kowane aiki.

Ya zuwa yanzu mata da yawan sukan zo ofishin su don gabatar da matsalar su, sun fi samun natsuwa wajen magana da ita fiye da yadda zasuyi magana da wasu mazan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG