Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Matashiya Mai Auren Jinsi Ta Harbe Matar


An harbe wata matashi da sukayi auren jinsi mai shekaru ashirin da tara (29) mai suna Felicia Dormans har lahira.

Laura Bluesstein, mai shekaru ashirin da takwas (28) da haihuwa mai zaman miji a auren nasu itace ta harbe matar a gidan su dake Mill street, Mount Holly, a jihar New Jersey, ta kasar Amurka.

Tuni dai ‘yan Sanda suka yi gaba da Laura, inda aka ajiyeta a gidan yari kafin a gurfanar da ita gaban kuliya.

Har yanzu dai ‘yan Sanda na kokarin sanin dalilin da yasa ta harbe matar koda yake bincike ya nuna cewa Bluestein, nada tarihin aikata muggan laifufuka da harkar kwaya wanda a baya aka yankemata hukunci akai a shekarun 2012 da 2014.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG