Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Guraben Karatu A Jami'o'in Kasar Amurka, Sun Karu Ina Mafita?


Baki daya kofofin makarantun gaba da sakandire har zuwa jami’o’I na kasar Amurka a bude suke. Muna maraba da duk wanda yake da sha’awar zuwa don karin ilimi, a kowane lokaci. Duk da kwararan matakai da gwamnati ta dauka wajen bada visa.

Hukumomi a ma’aikatar cikin gidan kasar Amurka, suka bayyar da hakan, a lokacin da yake bayani Mr. Rick Ruth a yayin wani taron karama juna sani, a ranar ilimi. Yace muna jinjinama ma’aikatan wannan ma’aikatar, da yadda suke gudanar da aikin su wajen ganin an taimakama dalibai daga kasashen duniya.

A ‘yan watannin baya ne gwamnatin kasar, ta saka takunkumi ga wasu kasashen musulamai shida 6, duk dai da cewar kotun kolin kasar bata aminta da tsarin ba, hakan kuma bai shafi tsarin bama dalibai damar shigowa don karin ilimi ba.

Yanzu haka dai zamu cigaba da daukar matakai kwarara, wajen ganin batagari basu yi amfani da wannan damar ba, wajen shigowa kasar don aikata aikin barna ba. Zamu kuma kokarta wajen ganin an bama dalibai dama don su shigo su samu ilimi.

A shekarar da ta gabata dalibai da suke zuwa kasar nan don neman ilimi, sun tallafawa tattalin arzikin kasar da kimanin kudi da suka haura dallar Amurka billiyan $32.8B. dai-dai na naira tiriliyan goma sha biyu N12T. Wannan ba karamin cigaba bane ga tattalin arzikin kasar mu.

Haka zalika duk wani dalibi da ya cika ka’idojin zuwa kasar nan don neman ilimi, zamu kokarta wajen bashi damar da ta dace, domin a yanzu haka manya manyan jami’o’I da sukayi fice a duniya, suna neman dalibai daga koina su cika takardun shiga zasu duba don basu guraben karatu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG