Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Na'ura Mai Bayyanar Da Mutun Ta Surar jiki A Germany


Hukumomi a kasar Germany sun kaddamar da wata sabuwar na’urar gwaji, na tsawon watanni shida, wadda zata dinga amfani da yanayin jikin mutun don bayyanar da ko wanene. Ita dai wannan na’urar za’a dinga amfani da itane, wajen magance ayyukan barna da ta’addanci.

Yadda na’urar zata dinga aiki shine, idan mutun ya taba zuwa wani wajen idan kyamara ta dauki hoton mutun, koda kuwa ya rufe fuskar shi, na’urar zata bayyanar da ko wanene, ta yadda jikin mutun yake ba lallai sai anga fuskar shi ba.

An dasa na’urar a tashar jirgin kasa dake babban birnin Berlin, inda mutane dari biyu 200, suka bada hotunan su da sunan su, don a yi gwaji da su a karon farko. A cewar ministan harkokin cikin gidan kasar Mr. Thomas De Maiziere, yace kimiyya da fasaha zasu zama hanya daya tilo da za’a iya magance duk wasu ayyukan barna a cikin al’ummah.

Ana sa ran idan wannan tsarin yayi nasara to sauran kasashe ma a duniya, zasu dauki wannan sabon salon, wajen gano mutane da suke barna a cikin al’ummah. Ita dai na’urar zata taimaka matuka wajen rage barna a duk inda aka saka na’urar kyamara da zata dinga daukar kaiwa da kawowar mutane.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG