Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Salo: Sabuwar Hanyar Tafiya Aiki Irinta Daya Tilo A Germany


A duk fadin duniya, bisa ga al’ada mutane kanyi tafiya musamman zuwa wajen ayyukan su, da suka shafi rayuwar su ta yau da kullun, kodai ta amfani da wani abun hawa da akafi sani.

Da dama mutane kanyi amfani da jirgin sama ko na kasa, mota, mashin, keke, da duk wani abu da ya saukaka ga mutun. Mr. Benjamin David, ya kafa tarihi a duniya.

Domin kuwa a irin nashi tunanin shine, ya gaji da shiga cikin jerin motoci da sauran abubuwan hawa don zuwa wajen aiki, da hakan kan bata mishi lokaci, kamun isa wajen aiki.

Hakan yasa shi fitowa da wata hanya da babu wani da zaiyi tunanin ta, don zuwa wajen aiki cikin sauri, batare da wani ya bata mishi rai ba. Kuma hanyar itace hanya daya tilo, da take tattare da kariya, lafiya da samun ingantacciyar lafiya a jiki.

Yayi amfani da wata jaka da ruwa baya iya shiga cikin ta, sai ya saka na’urar kwanfutar shi da agogon hannun shi, kana da wayar shi ciki. Sai ya tsunduma cikin ruwa yanata iyo, wanda yayi tafiyar da takai kimanin kilomita biyu, daga gidan shi zuwa wajen aikin shi.

Tsakanin gidan shi da wajen aikin shi, akwai wani rafi da ya ratsa kogin Isar a tsakiyar birnin Minich ta kasar Germany. Sau da yawa mutane kanyi mishi dariya, a yayin da yake iyo cikin ruwa.

Shi kuwa yakan maida musu da amsa cewar, wannan yafi saurin isa inda mutun zashi, kana da samun lafiya domin kuwa yana motsa jikin shi. Lallai kuwa tarihi ba zai manta da matafiyi cikin ruwa don zuwa wajen aiki ba, Mr. Benjamin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG