Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Na Yunkurin Samar Da Maganin Cutar Mantuwa


Sakamakon kididdigar wata kungiya mai fafutukar kariya ga cutar mantuwa, mai suna ‘Alzheimer’ a turance, sun iya gano cewar, kimanin mutane sama da milliyan arbain da hudu na dauke da wannan cutar a fadin duniya. Cutar dai na taba jijiyoyin kwakwalwa ne, inda take rage musu karfi, har ta kai ga mutun baya iya tuna komai.

Wasu masu bincike a jami’ar Glasgow dake kasar Scotland, a Jami’ar ‘Leister’ ta kasar Ingila sun samo maganin dake dakilar da matsalolin kwakwalwa, da suka shafi mantuwa. Maganin mai suna ‘Allosteric ligands’ na aiki ne domin farfado da sinadaran gina jiki ‘Protein’ dake kwakwalwa mai suna ‘Hippocampus’ a turance, wanda tasirin shi, a jikin dan adan ke raguwa yayin da cutar Alzheimer ke ci gaba da ta’azzara.

Wani masanin kwayar halittar dan adam dake jami’ar Glasgow, Farfesa Andrew Tobin, shine ya jagoranci aikin wannan kididdigar wacce aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ‘Clinical Investigation’ Farfesa Tobin, ya kara da cewar maganin na iya tsawaita rayuwar bera. Magungunan da ake amfani dasu, yanzu anyi su ne domin rage alamomin cutar, amma masu binciken sunce aikinsu yana maida hankali ne akan magance cutar gabaki daya.

Masu binciken sun yi gwajin maganin ne akan bera, inda suka saka mishi cutar ‘wild cow’ wacce take tamkar cutar mantuwa a jikin dan adam. Sakamakon nasu ya nuna alamun nasara, domin berayen da aka bawa magani, sun iya tuna abubuwan da suka wuce, kana wadanda kuma ba a bawa magani ba, basu iya tuna komai ba. Tobin ya kara da cewar, wannan ba magani ne na yanzu-yanzu ba, domin zai dauki kimanin shekaru biyar zuwa goma kafin a fara amfani da shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG