Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ware fam miliyan £150 don ganin ta sayo ‘yan wasa biyu Virgil Van Dijk na Southampton da kuma mai tsaron baya na Juventus Alex Sandros dan shekaru 26 a duniya.

Everton tace tana da kwarin Gwiwa wajan sayen dan wasan tsakiya na Swansea City, Sigurdsson inda ta ware fam miliyan £45, wajan ganin ta kawo shi kungiyarta.

Manchester United yanzu ta mai da hankalinta ne kan matashin dan wasan tsakiya na kasar Portugal mai taka leda a kungiyar Bayern Munich Renato Sanches dan shekara 19.

Lucas Perez na Arsenal yace yana son barin kungiyar kafin fara wasan kakar bana.

Chelsea ta ce zata cire ranta kan batun neman dan wasan tsakiya na Arsenal, Alex Chamberlain.

Shi kuwa dan wasan gaba na Barcelona Neymar, ya shaidawa takwarorinsa na kungiyar Lionel Messi da Luis Suarez cewa yana nan daram a Barcelona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG