Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zama Shahararriya Shine Babban Buri Na


Jamila Ado mai Wuka
Jamila Ado mai Wuka

Natsuwar rubuta wakoki tafi samuwa cikin dare in ji mawakiya Jamila Ado Mai wuka, ta furta haka ne a wata tattaunawa da wakiliyar muryar Amurka, Baraka Bashir, a birnin Kano.

Koda yake ta ce ta canza sheka zuwa harkar fina-finai a wani yunkurin na tabbatar da ta cika burinta na zama fitatciyar tauraruwa mai dogaro da kai.

Ta ce ta fara fina-finai ne bayan da ta lura banda waka harkar fim na daga cikin hanyoyin da mace zata iya wa’azantar da alumma inda ta ke cewa mutane sun bambanta inda wasu ta fim suke daukar sakonninsu yayin da wasu suke dauka ta waka.

Mai wuka ta kara da cewa waka na kawo kudin muddin mutum yana yawaita rera wakokin siyasa ko na biki, baya ga nan waka bata samar da kudaden shiga sai na lokaci zuwa lokaci.

Ko da yake ta ce babban burin ta bai wuce ta ga ta daukaka kowa ya santa ba sannan daga bisani sai ta yi aure.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG