Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau fim din da aka dade ana Jira Toilet Ek Prem Katha, na shahararren jarumin nan na Bollywood, Akshay Kumar, zai fito a Bollywood ta kasar Indiya.

Hukumomin Bollywood, sun yi amannan cewa wannan fim din zai taimakawa masana’anyar ta samu farfadowa dangane da batun samu kudaden shiga ganin cewa kawo yanzu masana’antar bata samu adaddin kudaden da ta sa ran cewa kawo yanzu sun shiga asusun masana’antar.

Rahotani na nuni da cewa an kashe kimanin dalar Amrka miliyan shida da dubu dari hudu (6,400,000) wajan hada wanna fim din kuma ana harsashen cewa a makon farko fim din zai samar da wannan adadin a saukake.

Akshay Kumar, yasan yadda yake shiga zukatan masoyan sa da irin abubuwan da suke bukata gani a fim, ta inda zasu samu annashiwa alokacin da suke kallo, saboda haka ya tanadesu a cikin wannan fim din domin farantawa maso kallo rai, shi yasa kowane lokaci ya fito da fim a Bollywood, jama’a ke tururuwa domin sun san kwaliya zata biya kudin sabulu.

Da yake tsokaci, Akshay Kumar, yace abun akwai armashi, domin kuwa kamar yadda suna Amir Khan, ya shiha zukatar mutane saboda irin fina finan da yake yi wanda yake gamsar da shima ya fara jindadin irin wanna daga masu kallo saboda irin nasa basirar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG