Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Da Real Madrid Zasu Gwabza


Manchester United da Real Madrid
Manchester United da Real Madrid

Kungiyoyin Manchester United da Real Madrid, a yau talata 8/8/2017 zasu kara a wasan Super Cup na yankin Turai na shekara 2017.

Kungiyoyin biyu zasu fafata ne sakamakon sune zakarun nahiyar na shekarar da ta wuce, 2016/17 Inda Real Madrid ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai, UEFA Champions League, da ci 4-1 akan Juventus.

Ita kuwa Manchester United itace wacce ta dauki kofin Europa League 2016/17,

inda ta doke Ajax da kwallo 2-1.

A tarihin haduwar kungiyoyin biyu tun kafuwarsu sun fafata sau 8 anyi kunnen doki sau 3 Real Madrid tayi nasara a wasanni 3, Manchester United kuwa ta doke Real a wasanni 2.

Sai kuma a yau inda zasu gwabza a karo na 9, Za'a fafata wannan wasan ne a filin wasa na Nacionalna Arena Filip, dake kasar Masadoniya da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar Kamaru da kasar Chadi, Inda harsashe ke nuna cewar Kowace kulob na iya samun nasa a wasan.

Real Madrid zatayi amfani da ‘yan wasanta irin su Cristiano Ronaldo, Modric, Benzema, da kuma Gareth Bale.

Ita kuwa Manchester United zata sa Sabin ‘yan wasan da ta sayo, a bana wanda suka hada da Romelu Lukaku, Victor Lindelof, Nemanja Matic da kuma dan wasan tsakiyarnan Paul Pogba,

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG