Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A yau Jumma'a za'a fara gasar Firimiya lig na Kasar Ingila, na shekara 2017/18

Inda kungiyoyin kwallon kafa su ashirin na cikin Ingila zasu fafata a tsakainsu wasannin za'a shafe mako talatin da takwas ana gwabzawa. A shekarar da ta gabata dai 2016/17 kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ita ta lashe gasar ta Firimiyar

A yau wasan za'a bude ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da takwararta ta Leicester City wace ta lashe gasar a shekara ta 2015/16,

Za'a buga wasan ne a filin wasa na Emirates mai daukan mutane 60,355 da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da kasar Chadi.

Ranar Asabar 12/8/2017 za'a buga tsakanin

Watford da Liverpool, Chelsea da Burnley, Crystal palace da Huddersfield Town, Everton da Stoke City, Southampton da Swansea City.

Sauran wasan sun hada da Westbromwich da AFC Bournemouth, Brighton & Hove da Manchester City,

Ranar Lahadi 13/8/2017 Newcastle da Tottenham, Manchester United da Westham United.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG