Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gareth Bale Ba Zai Sami Taka Leda Ba-Inji Zinedine Zidane


A cigaba da wasannin da akeyi na cin kofin kasashen nahiyar yankin Turai Uefa champions League, na shekara ta 2016/2017, a matakin wasan zagaye na goma sha shida, jiya kungiyar kwallon kafa ta PSG, dake kasar Faransa ta lallasa Barcelona, da kwallaye 4-0.

PSG, ta samu nasarar jefa kwallayenne a cikin minti 18 da 55 ta kafar dan wasanta Di Maria, a cikin minti na 40 kuwa Draxler, ya jefa tasa kwallon a raga, yayinda shi kuma Cavani, ya jefa kwallo ta hudu a cikin minti na 72 da fara wasan.

Benfica, kuwa ta doke Borussia Dortmund, da kwallo 1-0, haka kuma idan Allah ya kaimu ranar Laraba 8/3/2017 za'a sake karawa zagaye na biyu inda Barcelona zata karbi bakuncin PSG, Borussia Dortmund da Benfica.

A yau kuma Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ce zata kece raini tsakaninta da Napoli, Bayern Munich, zata karbi bakuncin Arsenal, za'a buga wasanne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.

Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, ya ce dan wasan gaba na kungiyar Gareth Bale, ba zai samu damar fafatawa a wasan da kungiyuarsa zata yi yau da Napoli ba Sakamakon bai jima da dawowa daga jinya ba.

Shi kuwa Ozil, na Arsenal, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta kan wasan da zasu yi da Bayern Munich, a yau cewar kungiyarsu Arsenal, tana da kwarin gwuiwar samun nasara a wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:32 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG