Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Sayar Da Riguna Na Fam miliyan £2.850,000


Wani bincike ya nuna ewar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, dake kasar Ingila har yanzu ita ke kan gaba wajan sayarda rigunan ‘yan wasan kwallon kafa a nahiyar kasashen Turai 2016.

Manchester united, tana daya daga cikin manya manyan Kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar turai dama duniya inda aka yi kiyasin a shekara ta dubu biyu da goma sha shida Manchester ta sayar da rigunan ‘yan wasanta na zunzurutun kudi har fam miliyan £2.850,000 a cikin 2016.

Wannan ya nuna cewa kungiyar ta haura kan takwarorinta irin su Real Madrid, ta Spain, wacce take mataki na biyu da ta sayar da na fam miliyan £2.290,000, sai Barcelona, a matsayi ta uku fam miliyan £1.980,000, Chelsea a mataki na hudu 1.650,000 Bayern Munic,h tana matsayi na biyar fam miliyan £1.500,000 Arsenal na shida fam miliyan £1.225,000.

Sauran sune Juventus, ta kasar Italiya a matsayi na bakwai da kudi fam dubu £850,000, akwai Liverpool ta takwas £705,000, Kungiyar kwallon kafa ta PSG, dake kasar faransa tana matsayi na tara da £685,000, ta karshe a cikin jerin kungiyoyi Goma itace AC Milan, da ta sayar da rigunan a shekara ta 2016 na kudi fam dubu £650,000

kiyasin ya nuna cewar Kungiyoyin kwallon kafa na kasar ingila sune mafi yawa a cikin jerin sunayen kungiyoyi goma inda suke da guda hudu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG