Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alaves Da Barcelona Zasu Kara A Wasan Karshe Na Copa Del Rey 2016/2017


A cigaba da fafatawa da akeyi ta Copa del rey a kasar Spain ta shekara 2016/2017 a matakin wasan kusa da karshe (Semi Final) a jiya kungiyar kwallon kafa ta Alaves ta doke Celta Vigo daci 1-0 a zagaye na biyu inda karawarsu ta farko suka tashi canjaras 0-0 wannan ya bada Dama ga Kungiyar ta Alaves, zuwa wasan karshe.

Alaves, zata gwabzane da takwararta ta Barcelona, a wasan Copa del rey na karshe ranar Asabar 27/5/2017.

A kasar Ingila kuwa a jiya Kungiyar Leicester City, ta lallasa Derby County, da kwallaye 3-1 a gasar cin kofin Kalu-Bale (FA Cup) na shekarar 2016/2017

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG