Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi 300 Zasu Fafata A Gasar Cin Kofin Gwamnan Gombe Talba Cup 2017


Talban Bauchi Cup
Talban Bauchi Cup

A yau za'a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta Mai girma Gwamnan jihar Gombe, Alh Ibrahim Hasan Dankwambo (Talban Gombe) Mai take Talba Cup 2017, karkashin jagorancin kungiyoyi masu fafatawa a lig lig wadanda ba kwararruba na jihar suka shirya.

Kungiyoyin sun shirya wannan ne don nuna farin ciki da Goyan bayansu bisa yadda Talban, yake taimakawa ta bangaren ciyar da harkar kwallon kafa a jihar dama wasu muhimman aiyuka a jihar ta Gombe.

Ana sa ran kungiyoyi guda dari uku daga kananan hukumomi goma sha daya na jihar zasu kece raini a tsakaninsu.

A yau dai za'a bude wasanne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Doma United, dake cikin garin Gombe, da takwararta ta Bare United, dake karamar hukumar Billiri, da misalin karfe Hudu na yamma a filin wasa na Fantami, dake Gombe,
babban bako a wajan shine Alhaji Ibrahim Hasan Dankwambo, Gwamnan Jihar
Za'a cigaba da sauran wasannin a wasu shiyoyin kananan hukumomin jihar.
Wasan zai kasance kihuwa dayane wato (Nock Out) akwai kyauta ta musamman ga duk Kungiyar da ta samu nasaran lashe wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:20 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG