Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Casa Watford A Wasannin Firimiya Lig


A ranar Asabar da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasara akan Hull City daci 2-0, Manchester united ta casa Watford da kwallaye 2-0

Westham tayi canjaras da Westbromwich 2-2, MiddleBrough 0-0, Everton Stoke City ta doke Crystal palace 1-0, Sunderland bata ji da dadiba a hannun Southampton da kwallo 4-0, Liverpool ta lallasa Tottenham daci 2-0.

A jiya lahadi kuma Burnley tayi kunnen doki 1-1 da Chelsea, Swansea City ta sha Leicester City kwallo 2-0.

A yau kuma za'a kece raini tsakanin AFC Bournemouth, da Manchester City, Zasu taka wasanni da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.

A saman teburin kuwa Kungiyar Chelsea take kan gaba da maki 60, Tottenham tana mataki na biyu da maki 50, sai Arsenal tana mataki na ukku itama da maki 50. Kasan teburin kuwa Hull City, tana mataki na goma sha takwas da maki 20, Crystal palace tana mataki na goma Sha tara da maki sha tara, sai Sunderland a mataki na ashirin itama da maki 19.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:03 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG