Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za'a Cigaba Da Gasar Wasannin UCL 2016/2017 Round 16


Yau talata 14, ga watan fabarairu, shekara ta 2017 za'a koma cigaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun nahiyar kasashen Turai Uefa champions league 2016/2017 a matakin wasan zagaye na goma sha shida (Round of Sixteen)

Wasan da za'a fara yau zai kasancene tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta PSG dake faransa da Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, dake kasar Spain, sai kuma kungirar Benfica, ta kasar Portugal, da Borussia Dortmund, ta kasar Jamus,
za'a buga wasaninne da misalin karfe tara Saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi, kuma sau uku kungiyar Barcelona tana samun nasara akan kungiyar PSG,

A jiya kuma a kasar Ingila an buga wasa daya tilo bangaren firimiya lig 2016/2017 mako na 25, AFC Bournemouth, ta sha kashi a hannun Manchester City da kwallo 2-0. Manchester City a yanzu tana matsayi na biyu a saman teburin da maki 52 Sakamakon nasarar da tasamu a jiya.

A can kasar Spain kuwa a wasannin La-liga 2016/2017 mako na 22 kungiyar Eibar ta lallasa takwaranta na Granada da kwallaye 4-0.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG