Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Kori Wasu Magoya Bayan Kungiyar Domin Nuna Wariyar Launin Fata


wasu magoya bayan Chelsea a jirgin kasa
wasu magoya bayan Chelsea a jirgin kasa

Kungiyar Chelsea ta kori wasu magoya bayan guda uku a yayinda take ci gaba da binciken al’amarin daya danganci nuna bambamcin launin fata daya faru a ranar Laraba.

A dauki wani bidiyo da nuna yadda wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar na turai suke ture wani bakar fata, a lokacin da magoya bayan kungiyar ke kan hanyar su ta zuwa kallon wasan Champion League da Chelsea zata kara da kungiyar PSG.

Bayan da suka ture mutumin, an ji magoya bayan kungiyar Chelsea na kururuta cewa “mu ‘yan nuna wariyar launin fatane, kuma muna son hakan.”

Kungiyar Chelsea dai ta gane mutane uku daga cikin mutanen da suka aikata wannan barna, harma ta dauki mataki nan take, kafin ta gudanar da karin bincike .

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar tace, kungiyar dai ta dakatar da wasu mutane uku daga zuwa filin kwallon ta na Stamford Bridge, a saboda sakamakon wani bincike da ta gudanar akan abiinda ya faru a cikin jirgin kasa da yammacin ranar talata data wuce, sanarwar ta cigaba da cewa idan har aka samu isasshen shedar cewa da hannun su a wannan al’amari, to kungiyar zata bada umarnin haramta musu shiga duk wani sha’anin kungiyar na har abada.

A yanzu haka dai, kungiyar tace, sun samu wasu ‘yan bayanai, kuma suna godiya ga magoya bayan kungiyar Chelsea da suka bayar da bayanai kan faruwar lamarin.

XS
SM
MD
LG