Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid na Cikin Matsala


Cristiano Ronaldo, (FILE PHOTO)
Cristiano Ronaldo, (FILE PHOTO)

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a kokarinta na cin gasar kwallon
kafa ta Zakarun Nahiyar Turai yazo mata da matsalolin ‘yan wasan da suka ji raunuka.

James Rodrigaz (ya karya kafarsa ta dama), Luka Modrik ma (ya karya kafar sa ta hagu ne), Pepe kuma ya sami rauni a (hakarkarin sa ne), sai kuma Fabio Coentrao (kafar sa ta hagu ce ta sami matsala),

Dan haka baza su sami buga wasan ranar laraba mai zuwa ba inda zasu yi karon batta da kulab din Schalke na kasar Jamus.

Baya ga Rodriguez, gagarumin harin da ‘yan wasan Madrid ke kaiwa yana nan a kasancewar Cristiano Ronaldo, Karim Benzema da kuma Gareth Bale na nan.

Bayen Munich ta maida wani gagarumin martani inda ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Hamburger SV. Da ci takwas da babu, wacce gagarumar nasara ce a cikin shekaru talatin da suka wuce.

“Ina matukar farin cikin yadda muka koma yanayin buga wasan mu na da” a cewar kocin Bayern Pep Guardiola gaf da tafiyar su inda zasu kara da kulab din Donetsk na Ukraine.

Real Madrid - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

XS
SM
MD
LG