Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo na Kalubalantar Lionel Messi


Ronaldo da Messi
Ronaldo da Messi

Bayan gano wani wasa mai ban shi’awa da fitaccen dan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo yayi a Jamus, dan kwallon a shirye yake da ya sake sabunta gwanintar sa domin kalubalantar Lionel Messi a gasar rukunin spaniya.

A laraba da ta gabata dai Ronaldo ya kai karshen wasanni uku da ya kasa taimakawa kulab din Madrid samun galaba kan Schalke a gasar zakarun turai.

A baiyane yake Cristiano Ronaldo ya ci kwallo, amma kocin Real Madrid Carlo Ancelotti yace “bazai taba zama mana matasala ba ko da dan wasan bai ci kwallo ba a wasu wassanni ba”. Amma ya tabbatar cewa yanzu kam kulab din ya koma dai dai kamar yadda suke da.

Kulab din Madrid dai ya jagoranci Barcelona da tazarar maki daya tak a gasar, kafin ziyartar da suka ka kai a Elche ranar lahadi.

Kulab din na Basalona dai ya sauki kulab din Malaga a ranar asabar kwana uku kafin tafiyar su wajan gasar zakarun turai a birnin Manchester.

##caption:Ronaldo da Messi##

XS
SM
MD
LG