Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Tsohon Dan Bangar Siyasa Na Kira Ga Matasa Su Yi Watsi Da Al'adar Banga


Wasu natsattsun matasa na taron ci gaba.
Wasu natsattsun matasa na taron ci gaba.

A rohotannin mu na yau na matasa masu dogaro da kai ta fannin ilimi, siyasa da zamantakewa. Filin ya tattauna ne da wani tsohon dan banga wanda yace shi kam yanzu kanshi yaw aye a game da bangar siyasa.

Wakiliyar VOA a wata hirar su, tsohon dan bangar ya kara da cewa “dage zaben da akayi a nasa ganin duk dabara ce ta yin magudin zabe domin gwamnati mai ci yanzu ta samu ta cigaba da mulki” .Ya kara da cewa a matsayin shi na tsohon dan banga yayi kojarin canza ma da yawan su ra’ayi da su bar bangar siyasa amma wasu sun gwammace su suyi ta wahala kan ‘yan canjin da basu taka kara sun karya ba.

Daga karshe ya fadi cewar yabar bangar siyasa dan baiga amfanin sa kansa cikin matsala ba kamar yadda ya tsallake rikijiya da baya a wani gangamin siyasa, ya kuma kara da cewar abokansa da yawa sun sha sara ba akan wani abin da ya taka kara ya karya ba.

Ya kuma yi kira ga matasa da kar su yarda a yaudare su amma su yi la’akari da cancanta musamman wanda zai ciyar da su gaba ta harkar ilimi da kuma ci gaban kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00
Direct link

##caption:Wasu natsattsun matasa na taron ci gaba.##

XS
SM
MD
LG