Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Shahararren Dan Wasan Real Madrid Na Sha'awar Tsaffin Kulab Din Shi


Shahararren Dan wasa Raul Gonzalez Blanco.
Shahararren Dan wasa Raul Gonzalez Blanco.

Shararren dan wasan gaban nan na kwallon kafa, Raul na sa ido akan gasar zakarun turai narukunin kulab 16 na baya bayan nan, tsakanin Real Madrid da Schalke 04 kuma yana son dukan tsaffin kulab dinsa su lashe gasannin shiyyarsu.

An fi son Real Madrid amma da alamun kulab din schalkke na iya lashe gasar. “Ra’ul dan shekaru 37 ya fada ma mujallar Goal cewa wurin horar da ‘yan wasa da ke New York a Hoftra “ya ba shi shi’awa. Zan so kulab din na schalke yayi nasara a Gelsenkirchen Madrid kuma ya yi nasara a Madrid. Hakan zai zama mafi alheri ma tawagar”.

Ana sa ran ganin tsohon dan wasan na gaba na spain wanda ke buga ma kulab din New York Cosmo wasa a yanzu da ya fara wasa a Real Madrid kafin ya koma kulab din schalke a shekarar 2014 ya kuma rattaba hannu a wani kwantaragi da kulab din Cosmo bayan sake farfadowar su.“Nayi yawancin aiki na ne a kulab din Real Madrid amma ina da shekaru biyu na musamman a schalke kuma ina kaunar kulab din matuka” inji Ra’ul.

Ana ma Ra’ul tayin dawo wa kulab din Real Madrid amma ba a matsayin dan wasa ba amma ya nuna cewar yana matukar shi’awar Bernabeu.

##caption:Shahararren Dan wasa Raul Gonzalez Blanco.##

XS
SM
MD
LG