Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Basu Cancanci Samun Nasarar Wasan Da Sukayi Da Malaga Ba


Spain Soccer Friendly
Spain Soccer Friendly

Luis Enrique, manajan kungiyar kwallon kafar Barcelona, yace basu cancanci samin nasarar wasan da sukayi da Malaga ranar asabar ba.

Juanmi ne dai ya buga kwallon da Dani Alves ya bugo masa, a inda ya jefa kwallon cikin raga, kwallon dai ta zamo itace kwallon da aka kawai aka jefa a raga a wasan.

Lashe Barcelona a wannan wasa shine ya kawo karshen nasarar da Barca’s tayi, na lashe wasa goma sha daya a jere a jere, kuma wannan shine damar da kungiyar ta kasa samu domin ta wuce takwarar wasar ta, kungiyar Real Madrid da take kan gaba a gasar La Liga.

Enrique dai yace, Malaga sunyi wasa na azo a gani kuma ya baiyana fatar ace wannan abun bai faru ba, amma dole ne nace an bamu kasha, kuma kila mun cancanci hakan.

A farkon wasan yayi, tunanin sunyi wasa mai kyau, amma Malaga sun yi amfani da damar da suka samu a kuskure daya da muka yi.

Mun fi maida hankali akan kwallo daga tsakiya, kuma ba muyi wani abin kirki ba a wasan, wadannan sune matsalolin mu.

XS
SM
MD
LG