Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Bai ji Dadi ba


Chelsea
Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake jar ragamar frimiya lik, bata ji da dadi ba a wasan da suka yi ya'u da kungiyar Burnley, inda suka yi kunnan doki.

Ben Mee, Ne yayi kwace-kwance ya jefawa kungiyar Burnley, kwallo, da kai, a lokacin da suka samu buga kwana, bayan da mai tsaron gidan Chelsea, Thibuat Courtois, ya ji wuta ya tura kwallon zuwa kwana.

Kwallon da kungiyar ta Burnley, ta jefawa Chelsea, yaso ne a minti na 81, wato saura minti 9, a tashi wasa.

Koch din Chelsea, Jose Mourinho, bai ji dadin yadda alkalin wasa ya hana su bugun daga kai sai mai tsaron gida ba, da a tsamanin shi Mourinho, din yakamata ace alkalin wasan ya basu.

##caption:Jose Mourinho##

XS
SM
MD
LG