Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Yanzu Sai Son Barka


Matasa a Nasarawa
Matasa a Nasarawa

Shuwagabanin al’uma , a jihar Nasarawa, sun bukaci jama’a, dasu koma gidajensu, sakamakon zaman lafiya da aka samu a jihar.

Yanayin zaman lafiyar, ya samu ne bayan ntaruruka da sarakunan gargajiya, na kabilu daban-daban suka gudanar da shugabanin Fulani, inda suka kuma ba junansu shawarwari, na fahimtar juna domin zaman lafiya.

Hakimin Fadamar Bauna, ta gabas daga kabilar Igon, Alhaji Ahmadu Adamu, yace hankula sun kwanta a yakuna daban-dabn dake bangarensa.

Shima sarkin kwandare, mai martaba Alhaji Ahmadu al Makura, yace duk da yake abubuwa da damas na bakin ciki sun afku a baya yanzu sun yi kokarin ganin jama’a, sun fahimci juna su kuma zauna tare.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah, reshen jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussain yace suna gargadin jama’arsu, kan su zauna lafiya, don haka yanzu sai son barka.

##:YANZU MATASA SAI SON BARKA##

XS
SM
MD
LG